Uncategorized

Ka Maida Hankali Kan Ayyukan Da Kake Yi Na Bunkasa Gombe Kar Ka Kula Hatsaniyar ‘Yan Adawa — Sheikh Albani Ga Inuwa

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Miyetti da ke cikin fadar Jihar Gombe, Sheikh Adam Muhammad Albani, ya bukaci Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, da ya ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan da aka dora masa, kada ya damu da soki burutsun ‘yan adawa gabanin babban zaben 2023 mai zuwa.

Sheikh Albani ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar da lakca ta watan Ramadan a masallacin Juma’a na Miyetti jiya Juma’a a garin Gombe. A yayin laccar wacce ta samu halartar Gwamna da sauran jami’an gwamnatin Jihar Gombe, Limamin ya tabbatarwa Gwamnan goyon bayansa.

Ya ce, “Musulunci ya koyar damu soyayya da goyon bayan shugaban da ya damu damu da gaske, kuma duba da saurarenmu da wannan gwamnan yake yi, mun yi imanin cewa ya damu da mu don haka za mu ci gaba da ba shi goyon baya a duk abin da zai yi”.

“Ba ma jiran sai ka yi ta yi mana bayyani game da ayyukan da kake yi don amfanin jihar mu da jama’an ta”, yana mai cewa “tabbas mutane za su koka musamman ma ‘yan adawa”.

Sheikh Albani ya yi kira ga al’ummar jihar su rika bai wa shugabannin su goyon baya da kuma yi musu addu’a domin shugabannin su iya kyautata musu.

Ya ce, “Babu wani shugaba ko gwamnati da za ta iya yin abin da ya dace ba tare da samun goyon bayan al’ummar ta ba, kuma mai girma Gwamna ba za ka taba aiwatar da shirye-shiryen ka a jihar nan ba idan ka ci gaba da sauraron suuka. Gwamna Inuwa namu ne kuma manufofinsa da shirye-shiryen sa don mu jama’a ya ke yin su,”.

A nasa bangaren, Gwamna Inuwa ya nemi goyon bayan al’ummar jihar su ci gaba da dabbaka zaman lafiya da ake samu a jihar.Ganin yadda kakar siyasa ta 2023 take kara karatowa, ya yi kira ga malaman addini da iyaye su mai da hankali wajen kara kula da ‘ya’yansu.

Ya kuma bukaci matasa a jihar su guji tashin hankali, su kuma koyi da’a da kamun kai a cikin al’umma, “kiran ya zama dole bisa la’akari da zabukan dake tafe wanda matasanmu ne manyan jiga-jigan ‘yan siyasa marasa kishin kasa ke amfani da su wajen haifar da tashin hankali da kawo cikas ga zaman lafiyan da muke mora”.

Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar su bada goyon baya don ci gaban jihar, “domin farfafo da kyakkyawan yanayin bada ilimi da sauran ayyukan more rayuwa ga kowa ba tare da la’akari da matsayin sa a cikin al’umma ba”.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Gombe Hon. Siddi Buba, da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, da Babban Sakataren Gwamna na musamman (PPS) Usman Kamara da sauran jami’an gwamnati.

Leave a Reply