Uncategorized

Kishi Kumallon Mata: Wata Mace Ta Kashe Kanta Saboda Mijinta Zai Kara Aure

Daga Khalid Idris Doya

Wata ‘yar kasuwa a jihar Kaduna, Misis Mary Ochugbede a ranar Juma’a ne ta kashe kanta da kanta kawai don minjinta na shirye-shiryen kara auren mata ta biyu.

Wata majiya daga iyalan mamaciyar ta shaida wa ‘yan jarida cewa Misis Mary ta fara soyayya da mijinta tun bayan da ya gama makarantar sakandari a shekarar 2000.

Majiyar ya kara da cewa Mary ta kammala jami’a a shekarar 1998 daga baya ta hadu da mijin nata a lokacin da shi ya kammala sakandari tare da shan alwashin cewa ita din za ta ba shi horon da zai kaisa ga shiga cikin jami’a tare da daukan nauyinsa kan hakan.

“Tana tsananin son mijinta wanda suka hadu a shekarar 2000 lokacin da ya gama sakandari. A daidai wannan lokacin da nake magana da kai yana kan matakin karatunsa na digiri na biyu. Wanda kuma ita ce ke daukan nauyin komainasa.”

Ya kara da cewa matar ta fara gano sauyin halin mijinta ne a lokacin da tag a yana yin wasu kiran waya a sirrance tare da boye mata da wacce yake waya.

“Kawarta ce ta fallasa abun da mijin ke boyewa inda ta sanar mata da shirin mijinta na kara wani sabon aure, ta sanar mata da rana da lokacin baiko. Ta jira har zuwa lokacin baikon inda ta tabbatar da mijin nata na soyayya da wata,” Inji majiyar.

Ya ce, bayan da ta gansu kuru-kuru, cikin gaggawa ta nausa zuwa gida inda ta kwankwadi wani sinadarin magani nan take ya jefar da ita shi kenan.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da aka masa don jin karin baya kan wannan lamarin ba.

Leave a Reply