Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Uku: Laduban Karanta Alkur’ani

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Abu ne sananne Alkur’ani maganar Allah ne, littafinsa ne da ya saukar wa Manzonsa a matsayin shiriya ga bayi a rayuwarsu gaba daya, ta bangaren Addini da Ibada da bangaren harkokin rayuwarsu. Shi ne mafificin littafin Allah, wanda ya saukar da shi ga mafificin Manzonsa (saw), ga al’umma mafi falala. Littafi ne wanda ya kunshi bayani, da shiriya, da haske, da rahma da albarka da waraka.

Littafi ne wanda Allah ya umurce mu mu karanta shi, mu yi tadabburinsa, mu fahimce shi, mu dauki ilimomin da suke cikinsa, mu yi aiki da shiriyoyinsa da umurni da haninsa da ke cikinsa.

Alkur’ani littafi ne mai girma, Allah ya siffanta shi da siffofi masu yawa, kuma masu girma, wadanda suke nuni a kan wajabcin girmama Alkur’ani, da yin ladabi wajen karanta shi, da nisantar wasa da wargi ko shagala wajen karanta shi. Saboda haka Malamai suka yi bayanin laduba na karanta Alkur’ani, wadanda za su sa mai karantawa ya yi tadabburin Alkur’anin, ya fahimci abin da yake karantawa, har ya samu falalan Alkur’anin wajen karanta shi, na samun natsuwa a zuciya, da warakar shubuhohi, da waraka a gangar jiki.

Daga cikin laduban karanta Alkur’ani, wajibi ne mutum ya yi niyya, kuma ya yi ikhlasi a cikin niyyar tasa, ya yi niyyar yin ibada ma Allah, da neman yardarsa, saboda karatun Alkur’ani ibada ce mai girma, ibada kuma ba ta karbuwa sai da ikhlasi. Shi ya sa Annabi (saw) ya ce: ((Ku karanta Alkur’ani, ku nemi yardar Allah, kafin wasu mutane su zo, suna saita shi kamar saita masu, suna gaggauta samun sakamakonsa ba sa jinkirta shi)). Ahmad (14855).
Ma’anar suna gaggauta sakamakonsa shi ne suna neman abin duniya da shi, na dukiya ko daukaka. Saboda haka wajibi ne mutum ya tsarkake karatunsa na Alkur’ani daga dukkan abin da zai bata masa ikhlasi.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani mutum ya karanta Alkur’ani yana mai tara hankalinsa a kansa, yana tadabburinsa, yana kallon ma’anoninsa, yana fahimtarsu, yana lura da su, yana kaskantar da kai ga ma’anonin maganar Allah, yana jin cewa; Allah yana magana ne da shi kai tsaye, saboda Alkur’ani maganar Allah ne.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so mutum idan zai yi karatun ya yi tsarki, saboda hakan yana cikin girmama maganar Allah. Kar mutum ya karanta Alkur’ani alhali yana da janaba har sai ya yi wanka, ko taimama idan ba zai iya amfani da ruwan ba, a dalilin rashin lafiya ko rashin ruwan. Amma mai janaba zai iya ambaton Allah, ya yi addu’a ya roke shi da addu’o’i na Alkur’ani.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so kar mutum ya yi karatu a wuraren kazanta, ko wuraren da ba za a saurara ma Alkur’anin ba, kamar wuraren hayaniya, saboda a cikin hakan akwai wulakanta Alkur’anin. Don haka bai halasta ya karanta shi a bayan gida wurin tsuguno ba, ko kan bola.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so mutum ya yi “Isti’aza”, ya ce: {A’uzu billahi minash shaidaninr rajeem}. Saboda Allah ya yi umurni da haka, inda ya ce: {Idan za ka karanta Alkur’ani to ka nemi tsari da Allah daga shaidan jifaffe} [al-Nahli: 98].
Zai yi haka ne don kar shaidan ya hana shi karatun, ko ya shagaltar da shi.
Haka ana so ya yi “basmala” ya ce: {Bismillahir rahmanir raheem} a farkon kowace sura, in ban da Suratu al-Taubah.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so mutum ya rera sautinsa, saboda ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Allah bai saurari wani abu ba kamar yadda ya saurari wani Annabi mai dadin murya, yana rera Alkur’ani, yana bayyana shi)). Bukhari (7544), Muslim (792).

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so mutum ya yi tartilinsa, wato ya karanta shi bisa ka’idojin Tajwidi. Allah ya ce: {Ka karanta Alkur’ani karantawa mai kyau} [al-Muzammil: 4].
Don haka ana so ya karanta shi a nitse, ba tare da sauri ba, tare da kiyaye ka’idojin karatu, da tsayar da harufansa da lafuzansa, don hakan zai sa mutum yin tadabburin ma’anoninsa.

Daga cikin laduban karatun Alkur’ani ana so mutum idan ya zo kan Ayoyin Sujada to ya tsaya ya yi sujuda, sai ya yi kabbara ya yi sujadan, ya yi tasbihi a cikinsa, sai ya dago ba tare da kabbara ba.

Lallai wannan wata na Ramadhan watan karatun Alkur’ani ne, ya kamata Mumini ya dage da yawaita karatun Alkur’ani a cikinsa, kuma ya lazimci wadannan laduba, don ya samu amfani da fa’idan karatun, ya samu albarkar Alkur’ani da rahmar da ke cikinsa, kuma don ya zama cikin wadanda Alkur’ani ceta a ranar Kiyama.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita karatun Alkur’ani a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu kishin al’umma da tausayin talakawa.

Leave a Reply