Uncategorized

2023: Mazabar Misau/Dambam Na Bukatar Shugabanci Na Kwarai, Inji Aftaka

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi

Mahmood Baballiya wanda aka fi sani da Aftaka ya bayyana cewa akwai kura-kurai a tsarin shugabancin da ake yi wa al’ummar mazabar Misau/Dambam. Wakilinmu ne ya zanta da shi ga kuma hirar kamar yadda aka yi ta:

BAUSHETIMES: Muna san sanin takaitaccen tarihin ka?

AFTAKA: Ni dai haifaffen garin Misau ne, a a ranar 02/02/1974 a gidan Alhaji Ahmadu Aftaka wato mahaifina marigayi ya yi dan majalisar jiha na mazabar Misau, amma ban zauna a wajen mahaifina ba, na tashi ne a wajen Baffana na rabu da mahaifina ya rasu kusan shekara arba’in ke nan yanzu.

Na yi makarantar Firamare a Kareu dake Yola ta jihar Adamawa da a shekara ta 1980 zuwa 1986, na ka yi Sakandare na a General Murtala Muhammed Yola/ Jimeta a shekara ta 1986 zuwa 1992 Sannan na tafi zuwa Jami’ar Maiduguri, bayan na gama na shiga harkar kasuwane ban taba aikin Gwamnati ba.

A Jami’ar Maiduguri na yi gwagwarmayar siyasa sosai misali na yi babban sakataren kungiyar daliban kimiyya da fasaha na Jami’ar, kuma ni ne farkon Amir na tsangayar Kimiyya na jami’ar, na yi shugaban sai kuma shugaban kwamitin tsare-tsare na musamman na kungiyar dalibai Musulmai na Jami’ar, na yi shugaban masu bada shawarwari na NUBASS da SUG na Jami’ar Maiduguri wannan kadan ne daga ciki.

BAUSHETIMES: An samu kiranye-kiranye a mazabar Misau/Dambam kan ka fito ka tsaya takara, kusan an kai ga gabar ka sayi Fom na tsayawa takarar kujerar Misau/Dambam, ko menene dalilin ka na kai ga wannan gaba?

AFTAKA: To da farko ita siyasa ana yin ta ne domin al’umma kuma duk dan siyasa da yake da burin cigaban al’ummarsa manufar sa da fa’idar sa shi ne domin ya nemo wa al’umma ko ‘yancin su ko hakkin su ko cigaban su, a iya tunanina wannan kujerar da muka jima muna nema, wanda mutane suka samu mu nema, na nemeta a shekara ta 2015 a karkashin jam’iyyar APC ban saya ba, na sake nema a shekara ta 2019 har-ila-yau a jam’iyyar APC Allah bai bani nasara ba a bara a cikin watan shida na bar jam’iyyar APC na koma jam’iyyar PDP a cikin tafiyar al’umma suka ga ya dace na sake tsayawa takarar domin na wakilce su.

Bayan tattaunawa da muhawarori da dama a halin yanzu na sayi Fom a karkashin jam’iyyar PDP domin yanzu muna fuskantar zaben fidda gwani. Insha Allah.

Daga cikin dalilai na da ya sa na ga cewa zan iya ko kuma na ga cewa zan shigo na bada gudumawa ta shine, ban gamsu da iya shugabancin da ake bayarwa a wannan kujera ba, idan mutum yana yawo yana kallon irin abubuwan da ke faruwa na zababbu a jihohi daban-daban na kasar nan zai yi takaicin abinda ke faruwa a mazabarmu na Misau/Dambam saboda haka shi ya sa na yi yunkurin na fito domin tafiyar da za mu yi, muna so mu canza tsarin siyasa da alkiblar siyasa da manufofin siyasa a Misau/Dambam, misali duk dan siyasar da za ka ji an ce ma wane ne, kamar Misau/Dambam, misali kamar ni za ka ji ana cewa Aftaka to mata da matasa ne suka mai dani har kowa ya sanni.

A a kodayaushe matasa su suke bada gudumawa kaso saba’in cikin dari na siyasa amma su ake tafiya a barsu a baya. To ni a cikin tsarina matasa su nake so a cikin tsarina duk abinda zamu samo su zamu amfanar cikin kashi saba’in, sannan dukkan wasu ababe da gwamnatin tarayya ke samar wa zamu kawo da kuma dukkan wasu hanyoyi da zababbu sukan bi domin kawo abubuwan cigaba a al’ummar su muma zamu yi kokari mu nemo domin amfanar da al’ummar mu insha Allahu Ta’alah.

BAUSHETIMES: Ganin yadda tsarin siyasa a yanzu ta gurbace ta zama siyar kudi, wanne irin hanyoyi za ka bi wajen fahimtar da al’umma saboda su fahimci siyasar kudi siyasa ce ta a tura mutum ya biyaku kuma in ya tafi bakwa kara ganin saba?

AFTAKA: To, idan kana cikin takara fahimtar da mutane kan wannan lamarin ai jama’a ba za su fahimceka ba, domin zansu ga kamar kana boye wa kan ka wani abu, domin siyasa duk wanda ya ce maka babu hidimar kudi karya ne, duk wanda ya ce maka siyasar Nijeriya ba da kudi ake yinta ba karya ne. Misali mu a jam’iyyar PDP mun sayi Fom duk dan takarar jam’iyyar PDP ya kashe mata naira miliyan biyu da naira dubu dari takwas har da na Jam’iyya naira dubu dari daya, ko anan aka tsaya dan takara ya kashe kudi, idan jama’a suka ce wanda ya zo ya kashe naira goma aka ce yafi wanda ya zo ya baku naira daya dacewa da kishi, a iya cewa sun bi daidai ko kuma su yi zaben tumun dare.

Ni kirana ga al’umma shi ne a zo a yi siyasa bisa hujjoji da manufofi, menene kake da shi gare mu in mun zabe ka me zakiyi mana? ba me zaka bamu ba, dole ka rike biyu abinda zaia yi mana idan ka samu kujera kafin abinda zaka bamu. Saboda haka wanne manufofi kake da shi gare mu a bangaren matasa, mata, hidimar noma da sauran su, wannan shine abinda ya dace al’umma su yi ta yadda idan dan takara ya zo sai ya fayyace muku abinda zai muku in ya kai ga gaci ku rubuta a rubuce, in ba haka ba yayi gaban sa.

BAUSHETIMES: Wanne kira kake da shi kan ‘Delegates’ masu zaben ‘yan takara a jam’iyyarku?

AFTAKA: Kira na ga jam’iyya da delegates shine abin da za ku iya yiwa al’umma shi ne fito da dan takara na gari amma zaben gama gari ba naku bane, idan kuka fito wa al’umma dan takara na gari kuma kun huta amma idan wanda bai cancanta ba ya kawo muku kudi ku karba amma ku zabi ra’ayin al’umma wanda ya dace.

BAUSHETIMES: Wanne Kira kake dashi ga Al’umma da Masu zabe?

AFTAKA: Daga karshe ina kira da roko ga ‘yan jam’iyya da al’ummar gari da a yi siyasa mai tsafta babu fada, babu zage-zage. kowanne dan Nijeriya yana da ‘yanci koda kanina ne ya wayi gari ya ce zai nemi kujerar da nake nema babu laifi babu cin mutunci a saboda haka a yi siyasan tsafta a rungumi juna a nemo wa al’umma maslaha wannan shine kirana ga al’umma.

Leave a Reply