Hausa

Kotun Ta Tabbatar Da Nasarar Inuwa Yahaya, Ka Na Ta Kori Ƙararrakin Jam’iyyar PDP Da ADC

 

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Gombe ta tabbatar da halascin sake zaɓen Gwamna Muhammadu InuwaYahaya, tare da yin watsi da ƙorafe-ƙorafen Jam’iyyar PDP dana ɗan takaranta Jibrin Barde, data jam’iyyar ADC da ɗan takararta Nafiu Bala waɗanda suka ƙalubalanci nasarar Inuwa Yahaya da mataimakinsa Manassah Daniel Jatau na Jam’iyyar APC.

A hukuncin da ya yanke, Kwamitin alƙalan kotun mai mambobi uku, ya yi watsi da ƙorafe-ƙorafen biyu saboda rashin hujjoji. 

Game da ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takararta suka shigar, kotun ta bayyanata a matsayin ƙara mai cike da rashin gaskiya, da rashin makama. 

PDP ta yi zargin cewa an tabka kura-kurai a zaɓen, kuma ba a zaɓi Inuwa Yahaya da mafi rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa ba. 

Kotun ta yi watsi da ƙarar ne saboda gazawar masu shigar da ƙarar wajen bada shedu da hujjoji kwarara. 

Tun farko da take yanke hukunci kan ƙarar Jam’iyyar ADC, wadda mai shari’a S.B Belgore ya karanto a madadin kwamitin alƙalan mai mutane uku, kotun ta ce koken na Jam’iyyar ADC da ɗan takaranta ba su da makama, don haka kotun ta yi watsi da su. 

ADC dai na ƙalubalantar ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wadda ya lashe zaben ne bisa zargin saɓanin sunaye a takardar shaidar mataimakinsa, ba tare da gabatar da wata hujja mai sahihanci ba. 

Kotun ta ƙalubalanci lamarin, inda ta ce batu ne da ya shafi al’amuran gabanin zaɓe, kuma mataimakin nasa ya cika mafi ƙarancin abinda ake buƙata na tsayawa takara. 

Dangane da zargin da ADC ta yi kan baiwa masu kaɗa kuri’a kuɗi, da cin hanci da rashawa da kuma rashin bin dokar zaɓe, kotun ta ce zarge-zargen wani dogon turanci ne kawai maras kan gado, domin mai shigar da ƙarar ya kasa tantancewa ko bada hujja guda ɗaya kan zargin da yake yi cewa an tafka magudi. 

Alkalin ya ce “Na tabbatar da cewa koken da jam’iyyar ADC ta shigar na ƙalubalantar nasarar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Gombe ba ta da wani tushe a kowane fanni kuma zaɓen waɗanda ake ƙara na ɗaya dana biyu a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan ga watan Maris yana da inganci kuma halastacce ne”.

Leave a Reply