Uncategorized

Lokaci Ya Yi Da Za Mu Gina Sabuwar Nijeriya: Tambuwal Ne Kuma Amsa


Ya ku wakilai masu zaben ‘yan takara a jam’iyyarmu ta PDP. Ina son na ja hankalinku akan wani abu da yake damunmu na rashin kyakykyawan shugabanci, domin kuwa a yanzu muna daf da yin zabe.


Gabanin babban zabe na kasa da za a gudanar, mun lura da yawan ‘yan takarkarun da muke da su. Wanda abin ke neman zama wani tsari na daban, inda mutane da daman ke neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun siyasa.


Yayin da iyayen gidan siyasa da dama ke da dama da ke yunkurin dafe takarar kujerar shugabancin kasar ke lallabar masu zaben fidda gwani a ko’ina, kowanne za a iya yi masa hukunci da irin abubuwan alkhairan da ya aikata a baya.
Yanzu kan kowa ya waye, an san masu san ci gaba da kuma masu mayar damu baya. Ba sabon labari ba ne yadda abubuwa suka cakude a kasar nan, wanda ake bukatar jajirtaccen shugaban da zai fuskancesu a karkashin tutar jam’iyyar PDP, domin ya yi mata takarar shugaban kasa.


In dai maganar jajirtaccen mutum ake wanda zai tserar da Nijeriya daga halin kuncin da take ciki, to ba a bukatar wani dogon nazari, domin kuwa Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kadai zai iya wannan namijin aikin. Domin kuwa kowa ya shaida irin kalubalen da ake fuskanta a kasar nan. 


Saboda haka akwai bukatar a fara bayyana jajirtattu irinsu. Kuma hanyoyin maganta matsalolinmu a bayyane suke, inda mafi yawansu ma suna nan rubuce cikin ma’aikatu da dama na gwamnatoci. An gaza aiwatar da su ne saboda saboda gazawar shugabanci.


Duk da wannan tarin kalubalen, jam’iyyar PDP ta yi rashin nasara a zabukan shugaban kasa guda biyu da suka wuce a tsahon shekaru bakwai da suka gabata, yanzu kuwa dama ta samu da za a zabi nagartaccen dan takara da zai iya fuskantar jam’iyya mai mulki har ma a samu nasara, wanda Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kadai zai iya yin wannan namijin kokarin.


Me ya sa muka ce Tambuwal ya chanchanta?
Idan ka dauke kasancewar Tambuwal na matsayin kwararren lauya, jajirtaccen mai hidimtawa al’umma, haka nan kuma masanin bangarorin gwamnati na zartarwa da majalisa.
Ya kasance mutum mai nagarta da kyawawan halaye sama da zango biyu da yayi a harkokin siyasa. Yanzu da kawunan ‘yan Nijeriya suka rarraba fiye da ko yaushe, jam’iyyar PDP na bukatar dan takarar da zai zama karbabbe a kowanne yanki na kasar nan, wanda ya zaga kowanne loko da sako a zamansa na tsohon kakakin majalisar wakilai ta ƙasa. Shi ne zai iya daukar kowanne nauyi na kasar nan kamar yadda ya dauki nauyin dukkanin ayyukan majalisa ta 7.


A bangaren tsaro kuwa, zai iya fuskantar kowanne kalubale, kamar yadda ya yaki na jihar, inda ya saka hannu akan dokar kalubalen tsaro, tare da samar da motoci 500, babura 765, gidaje 132 ga jami’an tsaro na kasa, ban da man zubawa a ababen hawan da kuma alawus dinsu.Saboda haka ya fahimci matsalar tsaron kasar nan kuma zai yi aiki da masu ruwa da tsaki a lamarin da samar da kayan aiki, domin a yaki abin a fadin kasa gaba daya.


Yajin aiki malaman jami’a ya zamo ruwan dare, inda malaman kwalejoji ke shirin bin bayansu. Inda gwamnatin tarayya ta yi biris da harkokin ilmi wanda ya zamo kashin bayan kowanne abu.
Saboda haka da zarar ya dare shugabancin kasar nan zai kawar da wannan, domin kuwa yanzu haka yana ware kaso 29% ga bangaren ilmi a kasafin kudin jihar Sokoto.


Dukkanin wasu kalubale da ake fuskanta a kasar nan, ana bukatar jajirtaccen shugaba wanda ba zai dinga shugabantar kasar daga asibiti ba, wanda Tambuwal yana da kosashshiyar lafiya, kuma bai tsufa ba, domin shekarunsa 56 ne kacal.


Sako daga: PRINCE DANIEL, arpa
Spokesperson

Tambuwal Campaign Organization (TCO)

Leave a Reply