Uncategorized

Ma’aijin PDP Na Arewa Maso Gabas Ya Fice Daga Jam’iyyar Bisa Zargin Rashin Adalci Ga Wike

By Khalid Idris Doya 

Ma’ajin jam’iyyar PDP a shiyyar arewa maso gabas, Hon. Galadima Abba Itas ya fice daga jam’iyyar tare da yasar da katin shaidar zamansa mambar jam’iyyar a jihar Bauchi bisa abun da ya zarga na rashin adalci wa gwamnan Ribas Nyesom Wike.

A wasikar fita daga jam’iyya da ya aike wa shugaban PDP a gundumar Itas da ke karamar hukumar Itas/Gadau a jihar Bauchi wanda muka ci karo da kwafinta, Hon. Abba ya shaida cewar ajiye shaidar zama dan jam’iyyar ya biyo bayan shawara da tuntubar masu ruwa da tsaki a siyasance da kuma abokai ne, inda suka amince masa da ya dauki wannan matakin.

Hon. Galadima Abba ya danganta ficewarsa daga PDP bisa abun da ya kira rashin adalcin da jam’iyyar ta yi wa gwamnan jihar Ribas Barista Nyesom Ezenwo Wike gabanin da kuma bayan zaben fitar da gwanin dan takarar shugaban kasa.

“Don haka zabin da aka yi wa Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na PDP sun saba wa ka’idojin siyasana da kuma akidata don haka na ga dacewar fita daga jam’iyar,” Inji Abba.

Ya ce, a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, ya gano cewa, rashin adalci ga mambobin da suka kafa jam’iyyar na barazana ga siyasar jagororin jam’iyyar a kashin kansu, don haka ya zama masa dole ya fice daga jam’iyyar domin nuna rashin gamsuwarsa bisa abubuwan da ake yin a rashin adalci a cikin PDP.

A cewarsa, halin da ake ciki a jam’iyyar PDP na matukar barazana ga yunkurin PDP na kwace mulki daga hannun APC a 2023, ya kuma gode da irin dammar da jam’iyyar ta ba shi, don haka ya shelanta wa duniya barin PDP.

Leave a Reply