Uncategorized

Nadada Zannan Misau Ya Gode Wa Wadanda Suka Halarci Daurin Auren ‘Ya’yansa

Muhammad Nadada Umar OON, (Zannan Misau) ya mika sakon godiya a madadinsa da iyalansa ga ‘yan uwa da abokan arzikin da suka samu damar halartar daurin auren ‘ya’yansa da aka gudanar a ranar Asabar 21 ga watan Mayun 2022 a cikin garin Bauchi.

Ya nuna godiyar tasa tare da fatan huta gajiya ga wadanda suka halarta tare da nuna musu so da kauna.

“Muna fatan kowa ya koma gida lafiya kuma muna godiya Allah ya bar zumunci, Allah ya bada ladan zumunci mun gode mun gode mun gode,” a cewar sakon da Muhammad Nadada Umar ya fitar a madadin iyalai.

Leave a Reply