Uncategorized

Raba Mata Da Maza A Sakandarin Jeka-Ka-Dawo Zai Magance Tabarbarewar Tarbiyyan Yara, Inji Kwamishinan Ilimin Bauchi


Daga Khalid Idris Doya
Kwamishinan Ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde ya bayyana cewar kudirin da suka bijiro da shi na raba makarantun sakandarin jeka-ka-dawo na mata zalla da na zama zalla zai taimaka sosai wajen shawo kan tabarbarewar tarbiyya da ke addabar al’umma a halin yanzu.


Kwamishinan a hirarsa ta musamman da wakilinmu ya kara da cewa muddin aka amince musu, hakan zai taimaka sosai wajen bai wa daliban ilimi da tarbiyya yadda ya kamata, yana mai cewa raba maza da matan zai kuma bai wa daliban damar maida hankali kan neman ilimin da suke zuwa makaranta domin shi.  


Kwamishinan yana mai cewa halin da ake ciki na tabarbarewar tarbiyya a tsakanin al’umma abu ne da ke bukatar a dauki matakin garanbawul domin tabbatar da al’umma ta gari, ya kuma ce cakuduwar daliban sakandari maza da mata a wannan lokacin na kara basu damar yin abubuwan da ka iya ruguza musu tarbiyya musamman lura da yadda kafafen sadarwar zamani suka yi tasiri wajen tallafa abubuwan badala a wannan lokaci.


Aliyu Usman Tilde ya kuma ce irin gabar da daliban sakandari ke kasancewa irin lokaci ne na tashen balaga wanda ke da matukar muhimmancin sanya ido kan daliban.


Ya ce, ma’aikatarsa ta koyarwa ce da tarbiyya, don haka ne ya ce daga cikin hakkokin al’umma a kansu shine su taya iyaye wajen tarbiyyan ‘ya’yansu musamman a gabar da suke hannunsu (Ma’aikaranta) ya nuna cewa dole ne su tabbatar wani abu mummuna bai samu dalibai a lokacin da suke cikin ajin daukan darasi ba balle su dauka su shiga da shi cikin al’umma.


A cewarsa: “Wannan nauyin da ke kanmu ya zama wajibi mu sauke kuma a yanzu din nan mu sauke lura da yadda abubuwa suka lalace.  
“Abubuwan da suke faruwa a makarantun da maza da mata ke hade ban isa fadinsu a nan ba; saboda hakan zai sanya wani Uban ya ma cire ‘yarsa daga makarantar boko har abada.


“Saboda lalacewar tarbiyya ta al’umma gaba daya, na biyu zuwan kafafen sadarwa sabbi na zamani sun shigo sun kara dakula lamura. Dabi’u sun shigo mana munana sun zo sun shige cikin wadannan yaran da suke gabar shekaru na hadari (Shekarun balaga) jikinsu na cancanzawa cikin hanzari ciki da waje sannan ba su san ma ya za su yi da wadannan canje-canjen ba har sai ya daukesu shekaru 4 zuwa 5 lokacin sun gama girma ko sun je jami’a ko sun yi aure sannan hankalinsu ya fara zuwa nan ne za su fara sanin abubuwan da ya kamata su yi da wanda bai kamata su yi ba.”


Kwamishinan ya yi tilawar cewa sama da shekara 40 kenan makarantun kwana suke rabe na maza daban na mata daban, don haka ne ya nuna cewa akwai bukatar makarantun jika-ka-dawo din ma a maidasu na maza zallla mata zalla domin kyautata tarbiyya. Ya mai cewa wannan tsarin ba wai sabo ba ne, lokacin da aka fara shi babu makarantun jeka-ka-dawo ne.


Ya ce irin matsalolin da suke samu na badala tsakanin daliban sakandarin maza da maza ba ya misaltuwa, don haka ne ma ya ce matsalolin suna nan jibge ne, ya kara da cewa malaman makaranta da shugabannin makarantu a kowani lokaci suna kokarin boye wasu abubuwan da suke faru.


“Malaman makaranta da shugabannin makaranta boye abubuwan da suke faruwa suke yi, ko kashi 10 ba su iya fada, ko nan ma’aikatar basu bari maganar ma ta iso. Dazu ina tattaunawa da wani malami kan abubuwan da aka yi a gabansa ya ma fi na wancan makarantar KAS Day, da muka gani ya tayar mana da hankali; ka san na ma KAS day din nan hoton farko da na gani daga Azare kuma fa, daga makarantar da shugaban makarantar shine daya daga cikin Firinsifal mafi kyawu namu.


“Yaran nan ranar da suka gama zana jarabawar kammala sakandari (NECO) shi kenan sai suka fito da wata al’ada cewa kowa zai fito da Maka (Alkami mai babbar baki) da tawadar alkamin sai na miji ya riga rubutu a jikin unifom din ‘yan ajinsu wadanda suka kammala jarabawa.


“Yaran suna jin sun ga makaranta a ranar ba abun da za a iya yi musu don haka sai su kangare. Aka nuna mana ga yara nan maza da mata a jikin junansu suna yi. Muka ce wannan abun menene haka?.


Kwamishinan ya cigaba da bayani da cewa; “Ba a jima ba sai ga shi an kawo mana hoton yarinya a bayyene a cikin makaranta ba wai a boye ba wannan ya nuna maka sauran ‘yan matan ma suna yin hakan. Ita wannan yarinyar haka ta kwaye hijabinta ta fitar da nononta a waje wani yaro ya zo yana rubutu a kan nonon.


“Wannan ba na son na gaya maka wasu abubuwa wanda malamai sun tabbatar sun shaida an yi a gabansu a makarantu daban-daban, yarinya ta daga hijabinta yaro ya shiga ciki ana cikin aji malami na koyarwa suna daga baya. Irin wadannan abubuwan an kama da dama suna yin irin wadannan abubuwan.


“Ko kuma a ce maka wasu shugabannin dalibai za su fito tun da sassafe karfe 6 sai a zo ana samun kwandom a cikin makaranta a tambayi mai gadi ya ce shi ba kowa yake kawowa rukunin yaran da suke zuwa tun da karfe shida; za su fada wa iyayensu cewa ana buqatarsu tun da safe don za su kula da yaran da suke zuwa a makare a she abun da suke yi kenan.


“To ta yaya za a yi mu muna nan a nan irin wadannan abubuwan suna faruwa sannan ba za mu tsayar da shi ba? Alhalin muna da halin da za mu iya yi. Ni da nake kan wannan kujerar ina da wuka ina da nama muddin aka bani dama na in tsayar da wannan aikin alfashan zan yi, wannan ne abun da muka tashi yi.”


Dakta Tilde ya ce tsarin zai fara ne daga ajin karamin sakandari har zuwa kammala sakandari, ya kuma ce sun samu goyon bayan masu ruwa da tsaki da dama.


Tilde ya kara da cewa tunin suka yi tsare-tsaren da suka dace wajen tabbatar da cewa muddin aka amince da wannan tsarin komai zai tafi yadda ya kamata domin za su raba makarantun ne daidai yadda ya kamata, a maimakon hakan ma sauki iyaye da daliban za su samu, a vangaren gwamnati kuma hakan ba zai ci kudi ba. Yana mai cewa a wasu unguwannin akwai makarantu biyu wasu sama da uku, don haka ne za su raba su ware na maza zalla da na mata zalla domin hankalin dalibai ya karkata zalla kan neman iliminsu.


Ya kuma kara da cewa za su yi la’akari wajen zaba wa mata makarantar da ke kusa da su, “Daman ba za ka tinkari gwamnanka da irin wannan abun har sai kai ka yi naka aikin, ka duba makarantu da dalibai, ka duba waye zaka tura ina waye za ka tura ina, ka ga eh abun yana iya yiyuwa.


“Alhamdullahi gwamnati tana da makarantun jeka-ka-dawo da yawa a jihar Bauchi, kusan kowace unguwa akwai makarantu guda biyu ko ma fiye, kawai sai mu dauki guda mu bai wa mata, wani kuma mu bai wa maza. A wasu guraren ma makarantun suna layi daya ne wata karanga ne kawai ta raba su. Yanzu ka xauki misali makarantar Sa’adu Zungur da Bakari Dukku guda biyu duk a kan layi daya suke karanga ce kawai ta raba su. Don haka mu muna bada shawara Sa’adu Zungur kaco-kam dinta sai ta zama ta ‘yan mata; Bakari Dukku guda biyu din nan dukka su zama na ‘yan maza.


“Da muka sanya lissafinmu muka ga hakan zai yi zai shiga tsaf. Sannan mun sake dubawa ma muka ga Sa’adu Zungur za ta iya daukan har da xaliban Barikin Sojoji.”
Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da su mara musu baya kan wannan kudurin nasu, yana mai cewa duk kokarin da suke yi shine don su tabbatar da ingancin ilimi da tarbiyyan xalibai a makatakin da ya dace daliban su samu tarbiyyar da ta dac

Leave a Reply