Uncategorized

Ramadan: Hon. Umar Attah Ya Gwangwaje Al’ummar Katagum Da Kayan Shan Ruwa Da Bude Baki

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi

Wani dan takaran kujeran Majalisan Wakilai ta tarayya a mazabar Katagum karkashin jam’iyyar APC, Hon Umar Attah babale ya raba buhunan kayan abinci wa shugabanin jam’iyyar APC a matakin gunduma da karamar hukuma domin saukaka musu a ciki wannan wata mai alfarma ta Ramadan.

Da ya ke jawabi a lokacin kaddamar da rabon, Hon. Attah ya ce ya yi wannan hobbasawar ne ga al’ummar yankin nasa domin saukaka musu a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan tare da faranta musu lura da muhimmancin da hakan ke da shi.

Umar ya kara da cewa a matsayinsa na dan jam’iyyar APC mai biyayya ya raba wasu daga cikin kayayyakin karkashin jam’iyyar APC, ya kara da cewa baya ga ‘yan jam’iyya ya kuma raba wasu kayayyakin wa sauran al’umma da abokan arziki musamman mabukata masu kananan karfi.

Ya yi kira ga shugabannin na jam’iyyar APC wadanda za su yi zaben fidda gwani da su yi kokari wajen fidda ‘yan takarar da suka dace domin samun nasarar jam’iyyar a lokacin babban zaben mai zuwa na 2023.

Daga karshe Attah ya ja hankalin al’umma su yi amfani da daman dayake cikin watan Ramadana wajen yin addu’o’in Allah ya bamu zaman lafiya a kasar nan da kwanciyan hankali.

Wasu da suka ci gajiyar shirin sun nuna godiya tare da fatan wasu ma za su yi koyi da irin wannan dabi’ar domin kyautata wa talakawa ko marasa karfi a cikin al’umma.

Leave a Reply