Sakkwatawa Ba Sa Goyon Bayan Kudurin Dokar Rage Karfin Sarkin
MusulmiSakkwatawan da suka halarci zaman sauraron ra’ayin jama’a akan kudurin dokar yiwa masarautar Mai alfarma Sarkin musulmi gyaran fuska da majalisar dokokin ta gabatar sun nuna adawa da kyamar wannan dokar.
Da yawa daga wakilan al’umma da suka halarci wannan zaman sun koka da rashin basu damar su bayyana ra’ayin su game da wannan dokar.
Sannan akasarin wadanda aka ba dama kamar tsohon dan majalisar wakilai kuma wakilin Kungiyar Sakkwatawa mu koma tushe Kakale Shuni, ya bayyana cewa idan dai har ba za a karawa Mai Alfarma Sarkin Musulumi karfin iko ba, to kuwa ba za a rage masa ba.
Shi ma da yake nasa bayani, wakilin Kungiyar Gidajen Sarauntar Sakkwato gaba dayan su Shehu Garba Takatuku, ya yi zargin cewa dukkanin wadanda aka ba damar suyi Magana ba ‘yan asalin jihar Sakkwato bane, dalibai ne da ke karatu a Sakkwato.
Don haka yace ba zasu taba amincewa da wannan matakin ba. Don haka yace ba za su taba amincewa da wannan kudurin ba, kuma zasu dauki akan dukkanin ‘yan siyasar dake wannan abun.
Shi kuma Magajin Garin Silame Alhaji Bandado Shehu Bande, duk da ance mutane su zo su bayyana ra’ayinsu, amma ba a basu dama ba, sun dai aikata abin da suke so, don haka ba da yawun Sakkwatawa za a gabatar da wannan dokar ba.
Tun da farko gwamnatin jihar ta ce zai yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.
An riga an yi wa dokar karatu na farko da na biyu a wani zama da aka yi ranar Talatar makon jiya, inda ake sa ran da ƙudurin ya zama doka, ƙarfin ikon nadawa da cire hakimai da dagatai zai koma ƙarƙashin ikon gwamnan jihar Sokoto, maimakon Sarkin Musulmi.
Dokar ta shafi damar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ke da ita, kan naɗa hakimai da dagatai kai tsaye, inda ikon hakan zai koma hannun gwamnan jihar da zarar dokar ta tabbata.
Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda jama’a da dama a Najeriya suka bayyana matakin da shirin rage ƙarfin ikon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.
Daga cikin waɗanda suka mayar da martini har da ƙungiyar Muslumi ta Najeriya Muric, da ta bayyana cewa taɓa kimar Sarkin Musulmin tamkar taba ruhin Musulman Najeriya ne