Uncategorized

Shugaban APC A Bauchi Ya Baiwa ‘Yan Sanda Kyautar Motar Sintiri A Misau

Daga Mohammed Kaka Misau

Alhaji Babayo Aliyu Misau, shugaban jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi ya yi kyautan Motar sintiri wa hukumar ‘yan sandan Nijeriya, da ke da zama a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchiauchi.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata takarda da aka raba wa manema labarai a jiya 21 ga watan mayu 2022 a garin Misau.

A cewar takarda, shugaban ya yi wannan kyautan ne da zimmar inganta ayyukan ‘yan sandan karamar hukumar domin ba su damar shiga lungu da sako don kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wannan mota ta samu ne da sa hannun sananniyar kungiyar nan CODOBA dake garin Misau.

Daga karshe sai ya yi kira ga hukumar da ta yi amfani da motar yadda ya kamata domin tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma.

Shi ma Kwmishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi ya yi godiya da wannan gudumawa sannan ya yi sauran jama’a su bada hadin kai wa ‘yan sanda dan samar da tsaro wa a
al’umma.

Leave a Reply