Shugaban APC: CONYIP Ta Ayyana Goyon Bayan Sanata Musa ‘313’
Wata hadakan kungiyar matasan Arewa ta siyasa wato ‘Coalition of Northern Youths in Politics’ (CONYIP) ta mara baya tare da zakulo Sanata Muhammad Sani Musa (313) kan ya zama sabon Shugaban jam’iyyar APC na kasa a yayin babban taron jam’iyyar da ke tafe a wata mai zuwa.
Kungiyar ta cikin sanarwar da suka fitar wa ‘yan jarida jimkadan bayan wata ganawa da suka yi a Bauchi, sun bayyana cewar tabbas Sanata Musa ya cancanta kuma ya dace a ba shi wannan damar lura da irin hidimar da ya yi wa jam’iyyar da fadi-tashin nema mata cigaba a kowani lokaci.
Shugaban kungiyar Injiniya Auwal M. Gotal ya ce, tabbas a irin wannan lokacin Sanata Sani Musa din ne ya fi dacewa da jagorancin APC lura da kwazonsa da gogewarsa a fagen siyasa da iya mu’amala da jama’a.
Sanata Sani Musa wanda mamba ne da ke wakiltar mazabar Neja ta Gabas a Majalisar dattabai, a cewar kungiyar shi ne mutumin da suka yi nazarin zai wanzar da zaman lafiya, hadin dai da jawo cigaba wa jam’iyyar muddin ya samu dama.
Kungiyar ta kara da cewa, sun kuma yi la’akari da kokarin Sanata Musa na jawo matasa a jika wajen gudanar da mulki tare, don haka suka dauki matsayar mara masa baya domin cigaban matasan Arewa da ma Nijeriya baki daya.
Gotal ya kara da cewa, “Mun amince da shi ne bisa damuwa da kishin jam’iyyar APC da mambobinta da yake yi a kowani lokaci wanda muka tabbatar in aka ba shi damar zai kyautata hadin kai da cigaban jam’iyyar, kuma hakan zai baiwa jam’iyyar gagarumar nasara a yayin babban zaben da ke tafe na 2023.”
A cewarsa, kungiyar tana da mambobi a jihohi a kalla 19, kuma sai da suka tuntubesu kafin daukar wannan matakin, ya na mai cewa sun kuma nemi shawarorin mata da matasa a Arewa inda suka amince da wannan matakin mara wa Sanata Musa baya.
Daga karshe kungiyar ta nemi masu ruwa da tsaki a APC da su baiwa Musa Muhammad dama domin farfado da APC da rike Mata kimarta.