Uncategorized

Shugaban Kasa 2023: Limamai Da Allarammomi Sun Gudanar Da Addu’o’i Kan Nasarar Gwamna Yahaya Bello A Bauchi

Hadakar kungiyoyin Limamai da Allarammomi sun gudanar da saukar Alkur’ani mai girma tare da gabatar da addu’o’i na musamman don rokon Allah (SWT) da ya baiwa gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello nasarar zama shugaban Nijeriya a yayin zaben 2023 da ke gabatowa.

Allarammomin da yawansu ya zarce 500 sun fito ne daga kananan hukumo 20 na jihar Bauchi, suna masu nuna matakin da suka dauka da cewa shine ya fi dacewa da irin lokacin da Nijeriya ke fuskantar babban zaben 2023 domin Allah ya kawo agajinsa cikin lamarin.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida yayin taron, daya daga cikin mahalarta Ustas Mubarak Mato Baba Karami, ya bayyana cewar Nijeriya tana bukatar matashi wanda ke da jini a jika da zai iya tunkarar dukkanin matsalolin da suka mamaye Nijeriya a halin yanzu.

Ya ce suna da tabbacin Yahaya Bello zai yi iyaka bakin kokarinsa don tabbatar da Nijeriya ta samu shugabanci na kwarai da zai iya daidaita abubuwan da suka garara gyaruwa.

Karami wanda kuma shine Shugaban kungiyar Limamai da masu wa’azi a jihar Bauchi, ya kara da cewa, “Babban abun da ya jawo hankalinmu wajen mara wa Yahaya Bello baya shine matashi dan uwanmu, a halin da Nijeriya ta ke ciki a yau muna bukatar matashi wanda zai kaimu ga tudun mun tsira. A baya dai mun yi ta neman canji sai Allah ya bar mu da dabararmu, amma yanzu muna ta kan yin addu’o’in neman nasara wa matashi da nufin Allah ya dafa masa ya iya gudanar da shugabanci na kwarai idan an zabeshi.

“Babban fatanmu da kwarin guiwarmu a kansa shine yadda ya kasance matashi. Kuma a ko’ina ka ji an ce maka matashi ka san yana da tunani mai inganci da zai iya gudanar da shugabanci na kwarai.”

Ya ce taron addu’o’in da suke yi zai taimaka sosai wa cigaban siyasar Nijeriya da al’umma, yana mai cewa Allah suke roka na ya tabbatar da alkairinsa da dacewarsa domin Nijeriya ta samu Shugaban da ya dace kuma ya cancanta da zai iya shawo kan matsalolin da suke addabar Nijeriya irinsu garkuwa da mutane, fashi da malamai, talauci, matsalar tattalin arziki da sauransu.

Shi ma a nasa fannin, Imam Sulaiman Abdullahi Azare, ya ce taron karanta Kur’ani da addu’o’in zai taimaka sosai wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, ya kara da cewa a gwada baiwa matashin Yahaya Bello dama domin ganin irin salon nashi jagorancin.

“Mutum ne matashi lafiyayye mai kaifin tunani da zai iya tsayuwa da tunaninsa ba da tunanin wasu ba, wanda kuma duk alamomi na shugabanci da nagarta yana da su, wannan ya sanya a matsayinmu na matasa muka ga ya kamata mu fito mu mara wa dan uwabmu matashi baya domin ganin damuwowin Nijeriya sun zama tarihi,” ya shaida.

Leave a Reply