Uncategorized

Zan Kula Da Matasa Da Harkar Ilimi Muddin Aka Zabeni, Inji Sabo

Daga Mohammed Kaka Misau

Mai neman tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai a mazabar Misau/Damban, Alhaji Sabo Ahmed ya sha alwashin cewa, muddin Allah ya ba shi nasara a zabe mai zuwa, zai fi maida hankali a fannin ingantaccen Ilimi da ababen cigaba wa mata da matasan mazabarsa.

Ahmed wanda ya fito neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya a Mazabar Misau da Dambam ta jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC, ya shaida hakan ne a lokacin da ke tattaunawa ta musamman da wakilinmu a gidansa da ke Dagauda, ya bayyana ilimi a matsayin wani sinadari da ke habaka kowace al’umma cikin hanzari.

Ya ce, “Ilimi tamkar gishirin rayuwa yake, har idan babu ilimi to la-shakka al’umma ba ta cigaba ba.”

Alhaji Ahmed wanda tsohon mai taimakawa na musamman kan harkar kungiyoyin agaji da ire-iren su wa tsohon gwamnan jihar Bauchi (Dakta) Mal. Isa Yuguda, har ila yau tsohon babban sakatare a fadar gwamnatin, Alhaji Ahmed ya ce mutane sun raja’a kan cewa makasudin neman ilimi shine don a samu aiki karkashin Gwamnati.

Ya ce hakika daukar aikin Gwamnati yana da wuya adadin dauka wanda ba kowane zai samu ba.

“Kafin Gwamnati ta dauki mutum dole sai ta masa tanadi na biyan shi hakkinsa wato albashi. Ya zama wajibi mu wayar da kan al’ummarmu cewa idan har suka nemi ilimi badan kawai su jira aikin Gwamnati ba, a’a yana da kyau su yi koyi ilimi domin ya share musu fage wajen koyan sana’o’in da za su dogara da kan su,” inji Alhaji Ahmed.

Ya ce ya zama masa wajibi ya fito neman wannnan kujera lura da yadda dimbim magoya bayan sa suka jima suna kiran sa da ya fito ya wakilce su domin ya kawo musu cigaban al’amura da zai inganta rayuwar su.

“Lura da yadda na rike bangarorin aiki da dama kuma nake da kwarewa akai, na ga ya zama abu ne mai kyau na amsa kiran al’umma ta na tsaya takara domin na bada tawa gudumawar ta hanyar kawo musu romon dimokuradiyya,” Inji Alhaji Ahmed.

Dan takarar majalisar wakilai ta tarayyar yac e yana da kudirori guda hudu Amma zaifi meda hankali kan daya daga ciki shine inganta rayuwar mata da matasa.

Ya kara da cewa “muna da mata da matasa masu tarin yawa a mazabata daga cikin su wasu sun samu ilimin boko wasu kuma basu samu damar yi ba, za mu yi kokarin mu samar da sana’o’i wa wadanda ba su samu damar yin karatu ba, wadanda suka sami ilimin boko kuma zamu nema musu aiki a Gwamnati ko kuma a masana’antu masu zaman kansu.”

Ya ce wanda ya samu damar yin aiki tare da gwamnoni har guda biyar ba tare da an taba samun wata matsala ba lallai yana da kwarewar da zai iya jagorantar mutanen sa.

Ya ce matasa na taka muhimmiyar rawa wajen cigaban al’umma, a saboda haka su da sauran al’umma ba za su zama kurar baya ba da zarar ya samu damar darewa kujerar a zaben shekara ta 2023.

Alhaji Ahmed ya ce lura da yawancin Al’ummar mazabar sa manoma ne, idan har ya yi nasara a wannan zabe zai yi iya kokarin sa wajen bibiyar dukkan wata hukumar da ta dace domin tabbatar da an bunkasa tafkin Maladumba wanda zai zama tamkar tafkin argungu dake jihar Kebbi, don inganta tattalin arzikin al’ummar Misau Damban har ma da jihar Bauchi baki daya.

“A karamar hukumar Dambam akwai want tafki wanda al’umma ke amfani da shi wajen noma amma a halin yanzu ya kafe, a saboda haka idan muka samu tattaunawa da hukumar da ta dace kan lamarin za mu samu damar farfadowa da dukkan su guda biyun,” dan takarar ya bada tabbaci kan hakan.

Ya kara da cewa idan ya samu dama zai samar da guraben karatu musamman na farnin lafiya wa al’ummar mazabar tasa ta yadda idan sun kammala da kansu zasu zo su rike manyan asibitocin yankin nasu.

Ya kira yi yayan jam’iyyar sa ta APC wadanda kishi ciyar da kasa ne a ransu da su zo su hada kai domin tabbatar da cewa an samu nasara a zaben shekara ta 2023.

Alhji Ahmed ya ce bai dace a ce siyasa hidimace ta a mutu ko a yi rai ba, ya bukaci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a mazabar Misau/ Damban da su ba shi dama wajen mara masa baya domin samun tikiti na jam’iyyar APC wanda da shi zai samu nasarar lashe zabe mai zuwa.

Leave a Reply