Uncategorized

Tarihin Gadar Jebba dake jihar Kwara.

Gadar Jebba, gada ta farko da turawan mulkin mallaka suka gina a Najeriya, wadda ta haɗe yankin Arewaci da Kudancin ƙasar.

Jebba, wani gari ne da ke jihar Kwara, a yammacin Najeriya. Garin ya ta’allaƙa ne a gaɓar kudancin kogin Neja (Niger River), mai nisan mil 550 (kilomita 885).

Jebba na cikin Ƙaramar Hukumar Moro. Kamar yadda ƙididdigar shekera ta 2006 ta nuna cewar, akwai al’umma 108,792, da ke rayuwa a yankin.

Al’ummar ƙabilar Nupe wadda mafi yawansu musulmai ne, suka kafa garin, waɗanda suka girka masarauta ƙarƙashin mulkin sarki Tsoede, wadda ya sake kafa garin ya kuma bunƙasa yankin a farkon ƙarni na 16.

Tsibirin Jebba da ke kogin Neja har yanzu akwai mazauna, wadda yawanci sun kasance al’ummar ƙabilar Nupe ƴan gargajiya.

Daga shekarun 1886 zuwa 1900, Jebba ita ce iyakar arewacin yankin da hukumomin ‘Royal Niger Company’ (Najeriya ta yau) ke gudanarwa.

Daga shekarar 1898 zuwa 1902 ta kasance hedikwatar rundunar Sir. Frederick Lugard, ta Yammacin Afirka (West African Frontier Force) kuma ta kasance hedikwatar turawan mulkin mallakar Burtaniya ta Arewacin Najeriya daga 1900 zuwa 1902.

Haka nan, an shimfiɗa titin jirgin ƙasa (Layin dogo) daga Legas zuwa Ibadan zuwa Jebba a shekarar 1909, kuma an danganta shi da Kano zuwa Baro ta hanyar gina gadar jirgin ƙasa mai tarago biyu (mai tsawon mita 547) a kan kogin Neja a 1915.

Wannan sabuwar hanyar layin dogo ta samar da ci gaban Jebba a matsayin cibiyar kasuwanci da sufuri. Dawa, masara, rogo, dawa, shinkafa, gero, da shanu, su ne manyan kayayyakin noma na garin.

Ana noman Rake a yankin a Bacita, kuma ana tace shi a masana’antar sukari da ke kusa.

Sana’o’in hannun Jebba na gida sun haɗa da saƙar auduga da ƙera tukwane. Haka kuma akwai masana’antar fasfo da takardu da ke cikin garin.

A shekarar 1984 aka kammala gina madatsar ruwa da wutar lantarki a Jebba a wani ɓangare na aikin madatsar ruwan Neja, wadda ya haɗa da Dam ɗin Kainji da ke samar da mafi yawan wutar lantarkin Najeriya.

An gina gadar babbar hanya mai layi huɗu a ƙarshen shekarun 1970 don ɗaukar babbar hanyar da ke sadarwa kudu zuwa arewa daga Legas.

Leave a Reply