Uncategorized

Wata Sabuwar Kungiyar Ta’addancin Ta Bullo A Nijeriya

Rahoto daga RFI Hausa ya labarto cewa; wata sabuwar kungiyar tsageru da ta kira kanta ‘Biafran Motherland Warrior’ ta bulla a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Rahotanni na cewa, wannan sabuwar kungiya ta fi ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra hatsari, yayin da ta kafa tungarta a yankin Mbaise.

Wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna membobin kungiyar na kaddamar da farmaki kan jami’an tsaro a yankin na Mbaise.

Tuni mazauna yankin suka fara zaman zullumi, inda kuma suka mika kukansu ga hukumomi don kare daga ayyukan kungiyar.

Kawo yanzu babu cikakkiyar masaniya kan manufar wannan kungiya, amma rahotanni sun ce, jami’an tsaro suke kai wa hare-hare.

One thought on “Wata Sabuwar Kungiyar Ta’addancin Ta Bullo A Nijeriya

Leave a Reply