Uncategorized

Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Yariman Gombe, Abdulkadir Abubakar

* Babban Rashi Muka Yi – Gwamna Inuwa

Daga Khalid Idris Doya

Da yammacin ranar Talata ne Allah ya yi rasuwa wa Yariman Gombe kuma Babban Hakimin Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar bayan gajeriyar rashin lafiya. 

Wakilinmu ya labarto cewa an yi masa jana’iza ne a ranar Laraba a fadar sarkin Gombe wadda Grand Khadi na jihar, Hon. Abdullahi Maikano Usman, ya jagoranta, inda daruruwan jama’a suka halarta ciki har da gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya, ‘yan majalisun jiha da na tarayya, sarakunan gargajiya da sauransu. 

Da yake mika sakon ta’aziyyarsa ga mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji (Dr) Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, da Majalisar Masarautar Gombe, da iyalan gidan sarautar Gombe, da dokacin al’ummar Jihar bisa wannan babban rashi, ya na mai addu’ar Allah Ta’ala ya gafartawa mamacin ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi. 

A sakonsa na ta’aziyya dauke da sanya hannun kakakinsa Ismaila Uba Misilli, gwamnan ya bayyana rasuwar basaraken a matsayin babban rashi ga Jihar Gombe da ƙasa baki ɗaya. 

Ya ce: “Wannan rashi ni aka yiwa. Yarima ya kasance uba kuma shugaba na kwarai abin koyi wanda ya kasance mai taimako da goyon bayan ci gaban al’ummarsa, wadda ya yi iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar a tsakanin al’umma”. 

Gwamna Inuwa ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen mutum mai hikima, wanda ya yi sarauta cikin mutunci da mutuntawa. 

Ya ce, “Marigayi Yarima mutum ne da ake mutuntawa sosai, wanda ya kasance abun koyi ga jama’a, kuma ya bar babban gibi da nagartattun hakayen da ba za a taɓa mantawa da su ba. Tabbas za mu yi kewar jagoranci da nasiharsa ta uba. 

“A tsawon shekarunsa na mulki a matsayin hakimi, an san Yarima da kokarin dabbaka zaman lafiya da nasiha kan haka, da fafutukar tabbatar da hadin kai da zaman lafiya, ba kawai a gundumarsa ta Gombe kadai ba, har ma a fadin Jihar Gombe baki daya. Za a ci gaba da tunawa da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ga al’ummarsa da Jihar Gombe a tsawon shekaru aru-aru. 

“A irin wannan mawuyacin lokaci, yana da kyau mu tuna da kyakkyawan tasirin da ya yi a cikin al’umma da kasa baki daya, kuma mu rika tunawa da shi ta hanyar dabbaka kyawawan abubuwan da ya bari na jagoranci da sadaukar da kai”.

Leave a Reply