Uncategorized

Buhari, Tinubu, Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni Da Ministoci Sun Halarci Auren Dan Gwamnan Gombe

 


Daga Khalid Idris Doya


Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amshi bakwancin muhimman mutane daga sassa daban-daban na kasar nan wadanda suka halarci jihar ta Gombe domin shaida daurin auren dansa, Arc. Misbahu Inuwa Yahaya wanda ya auri Barista Amina Babayo da ake wa lakabi da (Ameera).


Wakilinmu ya nakalto cewa babban Limamin masallacin Juma’a na Gombe, Sheikh Barista Ali Hammari shine ya jagoranci daurin auren a ranar Asabar. 


Mai Martaba Sarkin Gombe, Dr Abubakar Shehu Abubakar III shine waliyin ango, yayin da Alhaji Kawu Adamu Dan Malikin Gombe ya kasance waliyin amarya. 


Waliyin amaryar ya mika auren Ameera ne ga Sarkin Gombe ta hannun wakilinsa babban Hakimin cikin Gombe, Alhaji AbdulKadir Abubakar Umar bayan cika sharrudan daurin auren kan Sadaki dubu dari daya. 


Daga cikin wadanda suka shaida da halartar daurin auren da ya gudana a babban masallacin Juma’a na jihar Gombe, ya kunshi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wadda sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya jagoranci tawagar shugaban kasa.


Sauran manyan baki sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.


Kana auren ya hada fuskokin shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC, Sanata Atiku Bagudu, Gwamnonin Arewa Maso Gabas da suka hada da na jihar Adamawa, Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri, Borno; Farfesa Babagana Umara Zulum, Bauchi; Abdulkadir Bala Mohammed da gwamnan jihar Yobe; Hon Mai Mala Buni gami kuma da gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule. 


Kazalika, tsohon gwamnan Jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Saudu Ahmed Alkali, Gobir, ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Shugaban ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Baba Alkali, tsohon ministan FCT, Dakta Aliyu Modibbo Umar duk sun halarci daurin auren. 


A bangaren Malamai kuma akwai Sheikh Sani Yahaya Jingir Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatisunnah, tsoffin ‘yan takarar kujerar Sanatan na jam’iyyar PDP na jihar Gombe, Dr. Jamilu Ishiyaku Gwamna da Dr. Babayo Ardo gami da ‘yan uwa da abokan arziki da dama duk sun halarci daurin auren. 


Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe da mambobinsu, Babban Alkalin jihar, Grand Khadi, Alkalai, manyan ma’aikatan jihar Gombe da sakataren Gwamnatin jihar Gombe, Professor Ibrahim Abubakar Njodi ya jagoranta, Shugaban ma’aikatar fadar Gwamnatin jihar, Abubakar Inuwa Kari Sannan, sarakuna, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, ‘yan Majalisun duk an ga fuskokinsu a wajen daurin auren. 


A jawabinsa yayin liyafar murna da wannan auren, gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya nuna gayar farin ciki da godiya bisa yadda muhimman mutanen suka halarci wannan auren na dansa, ya ce tabbas ya ga karamci. 


Da suke fatan alkairi ga ma’auratan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Kashim Shettima da shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan sun taya ma’auratan murna tare da musu addu’ar Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a dayyiba.

Leave a Reply