More

FALLASA: Yadda Bello Matawalle Ya Kwashe Biliyoyi Da Sunan Aikin Tashar Jirgin Sama A Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fito da sabbin hujjoji na yadda tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi sama da faɗi da kuɗin aikin tashar jirgin sama.

A ranar Juma’ar makon jiya ne Matawalle ya musanta zargin sace biliyoyin kuɗi da sunan aikin jirgin saman.

A wata takardar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a cikin makon nan a Gusau, ta ce musanta “Wannan batu ba komi bane face rashin kunya da kuma kira wa kai fallasa.”

Ya ƙara da cewa, idan ma dai ban da Matawalle na ƙoƙarin wawitar da mutane, ya manta yadda a ranar 25 ga watan Oktoban 2021 ya kira waya ya bada umurni aka fitar da Naira biliyan ɗaya daga asusun Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, wanda a ciki ne aka tura wa ‘ɗan kwangilan aikin tashar jirgin sama Naira Miliyan 825.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta yi niyyar tanka wa mutumin da ake zargi da satar dukiyar al’umma ba. Sai dai kawai don a fayyace tsakanin gaskiya da ƙarya, musamman ma ganin cewa ya fito ya musanta zargin da ake yi masa.

“Babu makawa, satar rashin imanin da aka tafka da sunan samar da tashar jirgin sama a Zamfara ba komi ba ne idan ka kwatanta shi da irin manyan sace-sacen da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi.

“Tsabar ƙarya ne a ce wai kuɗin da ‘yan kwangila suka gabatar da farko ya kai biliyan 28, amma tsohuwar gwmanatin ta zaftare shi zuwa biliyan 11. Babu wani ɗan kwangila da zai Aminta a zaftare mishi kuɗin aiki da kaso 61% ba tare da asalin aikin ya taɓu ba. Wannan ya sa shakku a asalin aikin tun farko. Ko ba komi Matawalle ya fallasa mana nagartar ɗan kwangilan da suka kawo.

“Matawalle, ya yi iƙirarin cewa aikin na tashar jirgin sama wai an fara shi ne kan tsarin tallafin banki na ‘Contract Financing’. Wannan abin kunya har ina? Tsarin tallafin kuɗi da banki ke ba ɗan kwangila sunanshi ‘Contract Financing Facility’, shi kuma ana ƙulla shi ne tsakanin ɗan kwangila da banki, babu Ruwan gwamnati a ciki. Don haka tsagoron ƙarya ne.

“Sannan batun wai kuɗaɗen da aka biya ɗan kwangilan an yi sub isa sahalewar ma’aikatar da ke kula da ayyuka, shi ma ƙarya ne. Hujjojin da muke da su, kuma waɗanda muka saki a yau sun tabbatar da an biya kuɗin ne ba tare da bin duk wata ƙa’ida ba.

“Ko don tarihi yana da kyau a sani cewa, An biya ‘yan kwangilan kaso 30% na aikin a matsayin biyan farko, inda aka basu Naira Biliyan 3,465,569,736.90 daga asusun ma’aikatar kuɗi ta jiha a ranar 19 ga watan Yunin 2020.  

“A matsayin biya na biyu, an sake tura musu Naira biliyan 2, 310, 379, 824.60 daga asusun ma’aikatar kuɗin jiha a ranar 19 ga watan Yuni da sunan bashi (wanda babu wannan tsarin sam a ƙa’idar gudanarwa ta gwamnati). An sake tura musu Naira biliyan 825, 000, 000.00 daga asusun ma’aikatar ƙananan hukumomi a ranara 25 ga watan Oktoban 2021 a matsayin biya na uku. 

“Haka kuma batun da Matawalle ya yi na cewa ɗan kwangilan ya kammala wasu ayyukan da suka haɗa da hanyar tafiyan jirgi, magudanan ruwa, babbar ƙofar shiga Tashan jirgin duk ƙarya ne. Shi ma akwai hotunan mun sake su.

“Iƙirarin wai an kammala wasu daga cikin ayyukan da kaso 50% zuwa 100% ma ƙarya ne. Ai filin tashar jirgin na nan, duk wanda ke son gani da idonsa yana iya zuwa don ganin irin ɓarnar da Matawalle ya yi.

“Hujjojin da muke da su sun tabbatar da cewa hukumomin kula da tashoshin jirgi na tarayya irinsu NCAA da NAMA duk ba a shigar da su cikin lamarin ba a farko, wanda ya saɓa da ƙa’idar gudanarwa ta sashen sufurin jiragen sama. Da a ce da gaske tsohuwar gwamnatin Matawalle take da tun a wurin fitar da tsarin aikin tashar jirgin saman za su nemi sahhalewar waɗannan hukumomi.

“Muna so Matawalle ya yi wa duniya bayanin dalilin da ya sa ya biya ɗan kwangila zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 6.78 kan aikin da su kansu sun tabbatar da cewa iyakarsa kaso 30%. Wanda kuma yanzu aka yi watsi da shi.

“Gwamnatin Dauda Lawal ba shaci faɗi take fitarwa ba, hujjoji ne waɗanda kowannensu ke da takarda. Kwamitin amsan Mulki ya yi dogon nazari kan hulɗoɗin gwamnati, wanda rahoton wannan kwamiti na da matuƙar tada hankali.

“Da sannu za mu fitar wa da al’umma irin satar rashin imanin da Matawalle ya jagoranta a tsohuwar gwamnatinsa. Kuma babu ko tantama cewa duk waɗanda ke da hannu a irin waɗannan ayyuka na almundahana da babakere ba za su sha ba. Wannan ba komi ba ne daga cikin abubuwan takaicin da za mu fallasa wanda tsohuwar gwamnatin ta aikata.”

Leave a Reply