Uncategorized

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Da Makomar Ilimin Afirka

Daga Dr. Habib Awais Abubakar

Akwai wata shaida da ba za a iya tantama akan ta ba cewa tsarin ilimin Afirka, ko ma dai tsarin ilimin Nijeriya yana cikin tsaka mai wuya.

Duk da dimbin albarkatun dan Adam da na kasa da ke nahiyar Afirka, tare da dimbin Attajirai da ke da farin jini a duniya, amma batun ilimi a wannan bangare na duniya yana cikin mawuyacin hali.

Abin takaici ne a ce gwamnatocin da suke zuwa da masu hannu da shuni na Afirka da Nijeriya musamman ma na arewacin kasarnan ba su taka rawar gani ba wajen ceto yankin da al’ummarsa daga tsananin jahilci da talauci da ke barazana ga wargaza yankin.

Abin damuwa ne matuka ganin cewa masu rike da madafun iko suna damuwa ne kawai da jin dadin rayuwar ’yan’uwansu na kusa da dukiyar al’umma; wannan na daya daga cikin wasu ayyuka na son rai da dama da kuma karancin tunanin wasu da ke kan madafun iko wanda hakan ya janyo kusan durkushewar tsarin ilimin al’umma a Nijeriya.Gami da karawa, an samu wani matashi, mai kuzari, mai da hankali, mai kirkire-kirkire kuma jajirtaccen Farfesa mai suna Adamu Abubakar Gwarzo.

Yana da ƙwazo, ba shi da kabilanci, kuma mai samar da ci gaba ne da ke da tarihin yin abu cikin inganci. Cikin kasa da shekaru goma Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya samu nasarar kawo sauyi ga ilimi a yankin Hamadar Afrika ta yadda ya kai ga kafa kofa ga kowa da kowa, ta hanyar kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Jamhuriyyar Nijer a Maradi tare da shirye-shiryen bayar da tallafin karatu da dama.

Labarin Farfesa Gwarzo ba shi misaltuwa kuma mai ban mamaki ne. Matashin wanda ya fito daga Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwarzo a Kano, mutum ne da yake da sha’awar canza rayuwa da zamantakewa.

Cikin wayo ya fahimci cewa hanyar da ta fi dacewa ta karfafa dan Adam ita ce ta hanyar samar da ilimi musamman ga mutanen Afirka.

Dangane da inganci da kuma zama na duniya baki daya, Farfesa Gwarzo ya zama shugaba na farko na kungiyar Jami’o’in Afrika Masu Zaman Kansu (AAPU).

Manufar kawar da jahilci da talauci a Afirka ya fara samar da sakamako mai kyau. Ya samu nasarar kafa MAAUN a Maradi, Jamhuriyar Nijar tare da fara ayyukan ilimi a sabuwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya a Kano, a ranar 23 ga watan Mayu, 2022, sannan tare da samar da Jami’ar Franco-British International University (FBIU), dake Kaduna, da kuma Jami’ar Canada da MAAUN Togo da dai sauransu, Farfesa Gwarzo ya zama dan Nijeriya na farko da ya kafa rukunin Jami’o’i a nahiyar da ta fi kowacce girma kuma ta biyu a yawan al’umma a duniya.

Zan karkare wannan rubutu da wasu muhimman batutuwa guda uku da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ke ba da shawara a kai, wadannan batutuwa uku ne: ilimi mai inganci, kirkire-kirkire da kuma hada kai da kasashen duniya.

4 thoughts on “Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Da Makomar Ilimin Afirka

Leave a Reply