Uncategorized

Yadda yaƙin Yukiren zai shafi talakan Nijeriya

Daga Ado Abdullahi

Ƙasashen Rasha da Yukiren su ne suke samar da kashi 30 na alkamar da duniya take buƙata. Da kuma kashi 20 na masarar da duniya ke amfani da ita.

Hukumar Kula da Abinci ta Amurka ta yi ƙiyasin a banar nan ƙasar Yukiren ba za ta samar wa duniya da alkama kusan metric ton miliyan bakwai ba. Wanann ba ƙaramin adadi ba ne. Haka nan ita kanta ƙasar Yukiren ɗin ta hana fitar da duk wata alkama, acca, da shanu zuwa ƙasashen waje a dalilin wannan mamaya.

Ƙasar Rasha kawai a shekarar 2020 ta sayar wa da ƙasashen Afrika kayan abinci na kusa da Dalar Amurka miliyan uku, wanda kashi 48 cikin ɗari (48%), duk alkama ce.

Haka nan ƙasar Amurka ita ce ta fi kowace ƙasa sayen kayan abinci don tallafa wa wuraren da ke fama da rikici da annobar yunwa a duniya. Kuma rabin irin abincin da take saye, tana saya ne daga Rasha da Yukiren. Ke nan saboda wannan yaƙi dole ta juya akalar cinikinta zuwa wasu ƙasashen domin sayen kayan abincin. Wanda hakan zai ƙara tsauwala tashin farashin abinci a duniya.

Talakan Nijeriya zai fuskanci ƙarin farashin biredi , fulawa da taliya a dalilin abin da muka zayyano a sama. Wannan ya biyo bayan dogaro da ƙasar nan ta yi kacokan akan shigowa da alkama daga ƙasashen Turai.

Idan muka dubi ɓangaren samar da takin zamani kuwa, ƙasar Rasha ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa samar da sinadaren da ake haɗa takin zamani. Haƙiƙa dalilin wannan yaƙi farashin takin zamani zai yi matuƙar tsada a duniya wanda haka yana nufin tsadar kayan amfanin gona ke nan.

Wannan ba zai bar Nijeriya a baya ba, wajen fuskantar hauhawar farashin kayan da ake nomawa. Wannan kuma yana zuwa ne bayan ƙarin farashin da ake fama da shi saboda zuwan cutar korona da ta addabi duniya.

Farashin man fetur, man dizal da iskar gas ya fara tashin gwauron zabi, wanda yanzu gangar gurɓataccen mai ta kai Dala 139 a duniya. Inda farashin iskar gas ya riga ya ninka kuɗinsa. Abin da wannan yake nufi shi ne da a ce mu muke tace man da muke amfani da shi da sai mu ce lallai talaka zai sha jar miya, domin ƙasar za ta sami kuɗaɗen shiga masu yawa. Amma kash ! Tunda sayo tataccen mai muke a ƙasashen waje dole a sayo da tsada sa’annan a biya kuɗin tallafi da tsada. Ma’ana dai mu ba za mu ga alfanun tsadar man a duniya ba. Hasali ma ya ƙara tsada saboda ba lallai gwamnati ta jure biyan kuɗin tallafin ba.

Yadda abin zai shafi talaka shi ne ƙarin kuɗin sufuri zai ƙara wa kayan masarufi kuɗi. Kamfanini kuma za su ƙara kuɗin hajarsu saboda suna sayen man dizal da tsada domin sarrafa injinansu.

Kasar Misra ta tanadi alkama ga kamfanoninta na wajen watanni takwas masu zuwa domin a cike giɓin ƙarancin alkama da za ta samu saboda wannan bala’i da aka shiga. Kuma duk da haka ta hana fitar da taliyar da take sarrafa wa zuwa ƙasashen ƙetare. Duk domin talakawanta su wadatu da abinci a wannan shekarar.

Amma mu kash ! Shugabannimu sun shagaltu da batun zaɓen 2023 . Ba su ɗauki wani mataki domin sauƙaƙa wa talaka raɗaɗin da ake tsammanin zai tsunduma a ciki na tsadar kayan masarufi, saboda wannan yaƙi na Rasha da Yukiren ba.

Hatta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin Yukiren da Rasha zai haifar da bala’in yunwa a duniya. Ke nan fatanmu shi ne Allah Ya kawo ƙarshen yaƙin nan cikin ƙanƙanin lokaci. Ya kuma kare al’umma shiga mawuyacin hali.

3 thoughts on “Yadda yaƙin Yukiren zai shafi talakan Nijeriya

Leave a Reply