Mun Daura mikatin kawo karshen fasa Shaguna : Shugaban Kasuwar Misau

By: Mohammed kaka Misau, Bauchi.
Biyo bayan samun yawaitar Balle shagunan al’uma dama yi musu Satan kayayyaki, Hadaddiyar kungiyar yan kasuwa ta Misau Traders union and artisant Association karkashin jagorancin Alh Salihu Malam Ibrahim wanda akafi sani da Malam Malami ta gudanar da taron tattaunawa a ofishinta dake cikin babbar kasuwan Misau.

Acewar shugaban Hadaddiyar kungiyar, manufar gudanarda wannan taro itace, domin tattauna ne akan matsalan tsaro, da kuma irin yadda ake 6alle shagunan mutane ana musu sata a cikin kasuwar.

Salihu Ibrahim yace kungiya ta dauki nauyin daukan yan Vigelentees domin kare dukiyoyin Al’umma, kana kuma an tattauna yadda za’a dauki masu kula da kasuwan, da kuma yadda za’ana biyansu ladan aikin da zasuyi.

A yayin taron dai, shugaban karamar hukumar Misau Abubakar Ahmed ya bada nasa shawarwarin ta yadda idan akabi za’a samu sauki ta wannan fuskar,inda yace Gwamnatin jaha tayi Alkawari wa yan kasuwa cewa zata basu bashi kamar yadda Gwamnatin baya ta bayar a shelarata 2015 to 2019.

Har ilayau, ayayin taron dai, an kuma samu shawarwari masu matukar tasiri, kamar yadda dan Sandan yaki wato DPO ya bayar, wanda a cewarsa idan anbi insha Allah za’a samu saukin matsalar tsaro daya addabi wannan gari na Misau.

Daga cikin wadanda suka halarci wajen taron sun hada da Shugaban karamar hukumar Misau, Hon. Abubakar Ahmed Garkuwan Misau, DPO na Misau police station, Ma’aji na Jiha Alh Yahaya Lamido (AY LAMIDO STORE), sai Mataimakin shugaban yan kasuwa na shiyyar Bauchi ta tsakiya, Hon Danlami Abbakolo, sai kwo-odinatan jiha Nata’ala Usman PZ dadai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: