Uncategorized

Ta-faru-ta-kare: Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa, Tinubu Ya Shaida Wa Buhari

Daga Mohammed Kaka Misau, Bauchi.

An jima ana zura ido kan batun da ake ta rade-radin cewa jigon jam’iyyar APC Mista Bola Ahmed Tinubu zai fito neman shugabanci Nijeriya a 2023, lamarin ya tabbata domin a yau ne Tinubun ya shelanta muradinsa na fito neman takarar Shugaban kasa a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.

Tinubu wanda ya shaida hakan a lokacin da ya ziyarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari yau din nan a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, yana mai cewa yana da cakkakken natijar da zai iya jagorantar kasar nan muddin ya samu damar hakan.

Leave a Reply